'Yan gudun hijirar Sudan sun ce ba zasu dawo ba

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Yayin da Sudan ta Kudu ke murnar samun 'yancin kai bayan ballewa daga Sudan, dubban 'yan gudun Hijira ne da ke zaune a sansanin Kakuma na Kasar Kenya, ne suka sha alwashin ba za su koma gida ba.

Sansanin 'yan gudun Hijirar Kakuma da ke Arewacin Kenya, ya kasance wani waje da 'yan gudun Hijirar da su ka guje wa yakin da aka gwabza a Sudan ke zaune.

Sansanin waje ne da dubban 'yan gudun Hijirar Sudan su ke yi wa kallo a matsayin gida garesu.

Kuma tun lokacin da aka cimma yarjejeniya samun zaman lafiya tsakanin Sudan da sabuwar kasar Sudan ta Kudu, ake ta faman mayar da dubban mazauna sansanin na Kakuma Sudan ta Kudu.

Sai dai a lokacin da wakiliyar BBC, Caroline Karobia ta ziyarci sansanin a kwanakin baya, ta ce duk da yake akasarin mazauna sansanin na murnar samun 'yancin kai da Kasarsu ta yi, amma sun ce ba sa son komawa can.