Sudan ta kudu ta samu 'yancin kanta

Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir
Image caption Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir

An karanto kudirin 'yancin kan Sudan ta Kudu a gaban dubban jama'a dazu a Juba babban birnin kasar.

An daga tutur sabuwar kasar a kabarin John Garan wanda ya jagoranci yakin da kasar ta yi da Sudan.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir, ya rattaba hannu akan kundin tsarin mulkin kasar sannan ya dauki ranstuwar kama aiki.

Gwamnatin Sudan ta amince da sabuwar makwabciyar ta wato Sudan ta Kudu a matsayin kasa mai cin gashin kanta, amma kuma har yanzu akwai wasu batutuwa da za'a iya kai ruwa rana a kai a tsakaninsu.

Akwai tashe-tsashen hankulla a wani yankin kan iyakar kasasehn biyu da ake ja-in-ja akansa.

Sai dai a jawabin sa dazu a wurin bikin 'yancin kan kasar Sudan ta Kudu, Sakatare janar na majalisar dinkin Duniya, Ban ki Moon, ya yi kira ga bangorin biyua su san cewa yakamata suyi aiki tare.