Sudan ta Kudu ta samu 'yan cin kai!

A yau ne Jamhuriyar Sudan ta Kudu ta kasance sabuwar Kasa a duniya.

Sai dai a yayin da ake ta biki don murnar wannan gagarumar nasara da Kasar ta samu, biyo bayan shafe dimbin shekaru ana yakin basasa a Sudan, akwai manya- manyan kalubale da sabuwar Gwamnatin Sudan ta Kudu za ta fuskanta.

Tun tsakar daren jiya ne dai gab da cikar agogon babban birnin Kasar wato Juba karfe goma sha biyu, al'ummar da ke faman jiran tsammani su ka fara kirge.

Kasar Sudan ta Kudu wadda ta kasance sabuwar Kasa a duniya, ta kuma kasance Mamba ta 193 a Majalisar Dinkin Duniya.

Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon, ya aike da na sa sakon taya murnar, in da ya ke cewa ya yi murna domin shiga sahun Shugabannin Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya da Ministoci da kuma Shugaba Kiir wajen murnar samun 'yan cin kan Sudan ta Kudu.

Sai dai kuma da dama na yi wa sabuwar Jamhuriyar Sudan ta Kudu kallon daya daga cikin matalautan kasashe, musamman ma ganin irin dinbin kalubalen da ke gabanta, kama daga na ilimi ya zuwa lafiya, da ababen more rayuwa da ci gaban Kasar kan ta.

Tun dai bayan da Fadar Gwamnatin Sudan dake birnin Khartoum ta amince da 'yancin kan makwabciyar ta a hukumance, ta tabbatar da cewa 'yan sabuwar Kasar Sudan ta Kudu za su rasa shaidar su ta zama 'yan Kasar ta, wanda wannan na nufin katse musu damar samun duk wasu abubuwa da a baya za su iya mora daga gare ta.

Yanzu dai da yake lokaci ne na biki da murna, kusan za'a ce ba kowa ne zai damu da hangen me gaba za ta haifar ba.