'Yan darikar Tijjaniya na tunawa da shugabansu

Dubun dubatar musulmi mabiya darikar tijjaniyya daga kasashen Afrika daban daban ne suka hallara a birnin Sakkwaton Najeriya yau domin bikin murnar zagayoyar ranar haihuwar jagoran darikar na yammacin Afrika Sheikh Ibrahim Nyass karo na dari da goma sha biyu.

Darikar wadda Wani malami Sidi Ahmad Tijjani ya assasa a shekarar 1784 a kasar Aljeriya tana daya daga cikin darikun addinin musulunci mafi yawan mabiya a yammacin Afrika da yankin Maghreb.