Tashin Bam a garin Suleja

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A watan Afrailu ma an samu tashin bam a hukumar zabe dake garin Suleja.

A Najeriya, akalla mutane uku ne suka mutu, sannan wadansu suka jikkata a garin Suleja da ke jihar Naija sakamakon tashin da wani abu da ake zaton bam ne ya yi a harabar wani Coci da ke garin.

Shaidun gani da ido dai sun ce fashewar ta auku ne da goshin la'asar kuma karar fashewar ta razana mutanen da ke yankin.

Hukumomi dai sun tabbatar da aukuwar fashewar, sai dai sun kara da cewa babu wanda ya mutu, illa dai an samu wadanda suka jikkata.

Bayanan da BBC ta samu daga wajen mutanen da suka shaida abin da ya wakana dai , sun tabbatar da cewa, wani abu ne da ake kyautata zaton bam ne ya tashi a harabar cocin da ake kira All Christian Fellowship, da ke garin Suleja da misalin karfe uku da rabi na rana.

A cewarsu karar fashewar ta ja hankalin mutanen da ke yankin, har suka fara gudun mu tsira.

Ita dai rundunar 'yan sanda jihar Naija ta hannun kakakinta, Mr Richard Oguche ya shaidawa BBC cewa, sun samu labarin aukuwar fashewar, sai dai ya kara da cewa har yanzu ba su tabbatar da yawan mutanen da suka mutu ba.

Ya kara da cewa, da zarar sun tabbatar da abin da ya faru zasu yiwa BBC karin bayani.

Sai dai a sakon da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta aikewa BBC ta hannun kakakinta, Malam Yusha'u Shu'aibu, ya ce mutane hudu ne suka samu munanan raunuka sakamakon fashewar, Kuma an garzaya da su asibitin da ke Abuja.

Mutane da suka shaida abin da ya faru dai sun ce jami'an tsaro sun killace wajen da abin ya faru, kazalika mazauna garin Sulejan sun razana matuka.

Ko a watan Afirilun da ya gabata dai, sai da wadansu bama-bamai suka tashi a ofishin hukumar zabe da ke garin na Suleja, inda suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Hukumomi dai sun ce suna gudanar da bincike a kan tashin bama-baman, sai dai kawo yanzu basu fitar da sakamakon binciken ba.

Najeriya dai na fama da matsalolin rashin tsaro musamman a baya-bayan nan inda ake samun yawan tashin bama-bamai a kasar.