Manoman Kano sun kalubalanci gwamnatin da ta shude

Hakkin mallakar hoto AFP

A Jihar Kano dake arewacin Najeriya, gamayyar Kungiyoyin Manoma na Jihar sun dora alhakin rashin cin moriyar wani shirin baiwa manoma rance da Babban Bankin Kasar CBN ya fito da shi tun sama da shekaru biyu da suka gabata, a kan Gwamnatin Jihar da ta shude da kuma Bankin UBA.

A cewar gamayyar Kungiyoyin Manoman, babu ko da Manomi daya daga Jihar da ya amfana da ga shirin bunkasa noma da Bankin CBN ya ware zunzurutun kudi har Naira Biliyan Dari Biyu don rabawa Manoman Kasar bashi.

Wanda kuma a yanzu Babban Bankin ya ce an raba abinda ya haura Naira Biliyan Dari da Talatin, inda Manoma sama da dubu Saba'in su ka amfana.

Sai dai a nata bangaren tsohuwar Gwamnatin Jihar ta ce ta dauki matakin tabbatar da gaskiya ne wajen tantance su wa ya kamata su ci moriyar shirin.