Guterras zai gana da Gwamnatin Kenya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

A yau ne ake sa ran Shugaban Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya zai nemi Gwamnatin Kenya da ta amince da gina karin sansani a saboda masu tserowa matsanancin farin da ke addabar gabashin Nahiyar Afirka.

Antonio Guterres zai gana ne da Shugaban Kasar Kenya Mwai Kibaki a birnin Nairobi.

Kuma Kwamishinan zai nemi izinin kammala ginin wani babban sansanin 'yan gudun hijira da zai iya daukar akalla mutane dubu tamanin.

Sai dai kuma ita Kasar ta Kenya na shakkar gina sansanin domin kada a baiwa 'yan Somalia kwarin gwuiwar zama a kasar na din- din- din.

Shi dai Antonio Guterres bashi da ta cewa da ya wuce jinjinawa Gwamnatin Kenya, a saboda rawar da ta taka wajen kyale dubban 'yan gudun hijira da matsanancin fari ya sa suka tsero daga Somalia, su kasance a Kasar.

A lokacin da Mr. Guterres ya kai ziyara sansanin 'yan gudun hijira na Dadaab a Jiya Lahadi, ya bayyana cewa matsalar Somalia ta fi ta ko ina a duniya kamari.

Ya dai ce sam ba shi da shakkar cewa a Yau Somalia na fuskantar matsanancin bala'i da kan afkarwa bil adama.

A sansanin Dadaab, ya ga matalautan matalauta, mafiya rauni cikin marasa rauni a duniya.

Wasu da ga cikin 'yan gudun hijirar sun ce ba sa jin wani zai iya ci gaba da rayuwa a Somalia muddin aka sake kwashe tsawon wasu watanni biyu ana fama da matsalar fari.

Domin farin ya lakume komai da suke dashi, duk wanda ya yi kokarin ci gaba da zama a can, kamar ya so kashe kansa ne da gangan.

Sai dai kuma yanayin sansanin 'yan gudun hijirar ma ya fara munana a saboda cunkoson Jama'a.

Wannan ne kuma dalilin da ya sa Mr. Guterress zai gana da Shugaban Kasar Kenya domin kokarin shawo kan sa don ya amince da kammala gina makeken sansanin da aka faro a bara.

To sai dai kawo yanzu ginin na nan a matsayin kango, bayan da Gwamnatin Kenya ta ki amincewa da kammala shi.

Ga kasar ta Kenya dai, gina babban sansani a kasar na da matukar tsauri.

Duk da dai cewa suna so su taimakawa makwabtansu 'yan Nahiyar Afirka, su na kuma shakkar kada hakan ya baiwa dubban 'yan Somalia damar rashewa a can domin zama na dindindin.