'Yan gudun hijira na kara kwarara Kenya

Ana saran Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Anthonio Gutterress zai gana da shugaban kasar Kenya, Mwai Kibaki, don ganin an bude sabon sansani ga 'yan Somalia da farin kasar ya daidaita.

Sansanin wanda ake kira IFO two na kusa ne da sansanin Dadaab, wanda yanzu haka keda 'yan somalia dubu dari ukku da sittin.

'Yan Somalia dai sai kara zuwa sansanin sukeyi, kuma masu aikin agaji sunce wurin yacika ya makil da jama'a.