Nada mukarrabai a Najeriya ya janyo ce-ce-ku-ce

A Najeriya, wani batu da yanzu haka ke jan hankulan Jama'a shi ne nade- naden mukarrabai da Shugabanni ke yi, kama daga matakin Shugaban Kasa da Gwamnoni ya zuwa Shugabannin Kananan Hukumomi.

A cewar Shugabannin dai su na nada mukarraban ne domin su taimaka musu wajen gudanar da harkokin mulki.

To sai dai wasu masu lura da al'amurra a Najeriya na ganin a mafi yawan lokuta kwalliya ba ta biyan kudin sabulu, musamman idan akayi la'akari da kudaden da ake kashewa wajen daukar dawainiyar mukarraban Gwamnatocin.

Masana sun bayyana cewa kamar ana karawa me karfi, karfi ne, musamman idan aka yi la'akari da cewa ko da mukarraban ko ba bu su, Gwamnatoci za su iya tafiyar da aiyukan su.