An bude taron tattaunawa a Syria

syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tattaunawar Syria

Mataikankin shugaban Syria, Farouk Al Shara ya ce ya na fatan sannu a hankali kasarsa zata kasance mai bin tafarkin domokradiyya mai mutunta ra'ayoyi mabanbanta.

Yace: "bamu da wani zabin da ya wuce mu zauna mu tattauna saidai ko in muna so a cigaba da zubda jini kuma tattalin arzikin kasar ya shiga garari"

Mataimakin Shugaban kasar na jawabi ne a wurin wani taron kasa a Damascus babban birnin Syria.

Hukumommin kasar ne suka shirya taron wanda ya hada da jam'iyyar BAATH mai mulki, da 'yan adawa da sauran kungiyoyin matasa.

Sai dai akwai wasu manyan 'yan adawa da suka kauracewa taron suna cewa da wuya a yi wata tattaunawa mai ma'ana bayan ana cigaba da kashe masu zanga zanga.