Shugabar Gwamnatin Jamus za ta kai ziyara Afirka

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta ziyarci wasu Kasashen Nahiyar Afrika uku in da za ta tattauna akan batutuwan da su ka shafi hadin guiwa ta fuskar tattalin arziki.

Ana ganin ma wani abu da ga cikin abubuwan da za ta tattauna akai har da wanda ya shafi bangaren makamashi.

Ana sa ran wasu 'yan Kasuwa daga Jamus za su biyo ayarin Shugabar Gwamnatin a ziyarar kwanaki biyu ta za ta yi a Kasashen Kenya da Najeriya da kuma Angola.

Shugaba Merkel dai ta ce a Kasar Kenya, za su tattauna akan yadda za'a bunkasa fasahar kimiyya domin samar da makamashi daga hasken rana, wanda Jamus ta kware akan haka.

A Najeriya da Angola kuwa za'a duba yiwuwar samar da karin fasaha ne a bangaren mai.

Shugabar ta kara da cewa Jamus na da muradin taimakawa kasashen ne domin samun daidaito da kuma samar da hadin kai tsakanin su da Jamus.