Mutane suna yin kaura daga Maiduguri

A Maiduguri babban birnin jihar Borno arewacin Najeriya wasu mutane na ci gaba da yin kaura daga garin zuwa wasu jihohin.

Yanzu haka dai kanana da manyan tashohin mota na ta samun karin matafiya.

Mazauna birnin Maidugurin dai na kokawa ne da matsalar yawan hare haren bama bamai da na bindigar da ke ci gaba da faruwa a unguwannin nasu.

Abin da kuma ke sa suna fuskantar fushin jami'an sojin da suke zargin na cin zarafi da hallaka wadanda ba su ji ba su gani ba.

Sai dai rundunar hadin gwiwar samar da tsaron ta musanta ta ce, wannan zargi ne, inda ta ce galibin mazauna birnin ba sa ba su hadin kai wajen gudanar da binciken masu kai hare haren da take zargin, saboda suna tare da su ne.