Yau za'a rufe Jami'ar Maiduguri saboda rashin tsaro

A Najeriya, yanzu haka daliban Jami'ar Maiduguri sun fara tattara komatsan su domin fita daga harabar makarantar, kafin karfe goma sha biyu na ranar yau.

Wannan kuwa ya biyo bayan sanarwar da Hukumomin Gudanarwar Jami'ar su ka fitar na rufe makarantar da yammacin jiya.

Hukumar Gudanarwar Jami'ar dai ta ce ta dauki wannan mataki ne domin kokarin kare lafiya da rayukan dalibai, sakamakon kalubalen tsaro da ake ci gaba da fuskanta a birnin Maiduguri da wasu sassan Jihar Borno.

Rufe Jami'ar ta Maidugurin dai na zuwa ne a daidai lokacin da mazauna birnin da dama ke ci gaba da kaura zuwa wasu Jihohin.