Nana Rawlings ba ta amince da zaben fidda gwani ba

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nana tare da mijinta wato Jerry Rawlings

Uwargidan tsohon Shugaban kasar Ghana, Nana Konadu Agyeman Rawlings ta nuna rashin amincewarta da sakamakon zaben fidda gwanin da jama'iyar NDC mai mulkin kasar ta gudanar a kasar a karshen mako.

Shugaba John Atta Mills da Nana Konadu Agyemang Rawlings ne dai suka yi takara a zaben fidda wanda zai tsayawa jami'ar takara a zabe mai zuwa, inda shugaban kasar ya lashe zaben da sama da kashi casa'in da uku cikin dari .

Sai dai a wata hira da gidan radiyon Joy FM mai zaman kansa dake birnin Accra da safiyar yau, Kofi Adams, kakakin uwargidan tsohon shugaban kasar yace basu yadda da sakamakon zaben ba.

Nana Konadu Rawlings ta samu kashi 3.1% cikin dari na kuri'un da aka jefa a zaben da jam'iyyar National Democratic Congress wato NDC ta gudanar a babban birnin kasar Accra.

Jam'iyyar dai ta amince da Shugaba John Atta Mills' a matsayin wanda zai kara tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar.

Masana sun ce tsaya takarar da Nana ta yi wani kokari ne na nuna irin tasirin da majinta yake da shi a jam'iyyar.

Masu goyon bayanta dai sun alakanta rashin nasarar da tayi ga rashin yawan mata a deleget-deleget din da suka kada kuri'a.