'Yan sanda sun kama wani dan Majalisar Jihar Naija

A Jihar Naija da ke arewacin Najeriya, rundunar `Yan sandan Jihar ce ta tsare mai wakiltar Naija ta arewa a Majalisar Dattawan Kasar, Sanata Ibrahim Musa dan Jam`iyyar adawa ta CPC.

Rundunar 'Yan sandan ta kuma gurfanar da shi gaban kuliya.

Rundunar dai na zarginsa ne da yin wasu takardun biyan haraji na bogi.

Sai dai Jam`iyyar CPC ta yi zargin cewa Gwamnatin Jihar ce da wasu `Yan Siyasa ke amfani da Jami`an tsaro don su tozarta Sanatan.

A Najeriya dai masu rajin kare Demokuradiyya na kukan cewa har yanzu babu wani ci gaba da aka samu ta fuskar hakuri da juna a tsakanin `Yan siyasa, musamman ma abokan adawa.