Rupert Murdoch na fuskantar karin matsin lamba

Rupert Murdoch Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rupert Murdoch

Hamshakin attajirin nan, mai kafafen yada labarai, Rupert Murdoch, na fuskantar karin matsin lamba, yayinda ake samun karin zargin aikata ba daidai ba, kan wasu 'yan jaridar dake masa aiki na satar shiga wayoyin jama'a suna daukar bayanai.

BBC ta fahimci cewa wasu ma'aikatan komfanin sa sun biya wani dan sanda don ya basu bayanai akan wasu 'yan gidan sarautar Burtaniya.

Wannan lamari dai yayi sanadiyar durkushewar jaridar News of The World, daya daga jaridun da suka fi samar masa da riba.

Wadannan bayanai na fitowa ne, yayinda mataimakin praministan Birtaniya Nick Clegg ya bukaci Rupert Murdoch da ya sake nazari kan yunkurin sa na mallakar kampanin yada shirye shiryen talabijin na BSkyB, wanda ya fi kowanne kudi a Birtaniya.