Tunawa da musulman da aka kashe a Srebnica

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An kashe akalla musulmai dubu takwas a garin Srebrenica a shekarar 1995

Dubban mutane ne za su halarci wani taro a gabashin garin Srebnica domin jimamin kisa kyashin da Sojojin Serbia su ka yiwa Musulmai a Bosnia.

Za'a binne kimanin gawawaki dari shida ne a wajen garin bayan an tantancesu.

An tono gawawakin ne a wani babban kabari a shekarar da ta gabata.

Taron tunawa da wadanda aka kashe shine na farko da aka shirya tun bayan da aka kama wani janar din sojin Bosnia wato Ratko Mladic.

An dai zargi Mladic ne da bada umarnin kaddamarda kisan a shekarar 1995.

A yanzu haka dai ana tuhumarsa ne a babban kotun manya laifuka ta kasa da kasa dake birnin Hague a kasar Switzerland.