Kungiyar HRW ta ce ya kamata Obama ya binciki Bush

Kungiyar dake rajin kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch, ta yi kira ga Shugaba Obama da ya sa a binciki magabacin sa Shugaba Bush tare da mukarrabansa bisa zargin aikata muggan laifuka.

A wani rahoto da Kungiyar Human Rights Watch ta fitar mai shafuka 107, Kungiyar ta ce tana da cikakkiyar shaida da za ta sa a kaddamar da bincike akan Shugaba Bush da manyan mukarraban sa.

Kungiyar ta bayyana amfani da salon tatsar bayanai inda mutum zai ji kamar zai nutse a ruwa wanda aka fi sani da suna Waterboarding da kuma kafa sansanonin sirri na hukumar tsaro ta CIA da kuma kwasar wadanda ake tsare da su zuwa wasu kasashen, a matsayin cin zali.

Tun a baya ne dai Gwamnatin Shugaba Obama ta kaddamar da bincike kan mutuwar wasu mutane biyu da suka rasu a hannun Jami'an Hukumar leken asiri ta CIA.

Sai dai Kungiyar Human Rights Watch ta ce wannan ba zai wakilci sauran batutuwan da gwamnatin Shugaba Bush ta dauka a matsayin wadanda basu keta doka ba.

Binciken dai kamar yadda Kungiyar ta ce ya kamata a yi, sun hada har da irin yadda ake tafi da wadanda aka kama.

Shugaba Bush da mukarrabansa dai sun sha nanata kare kansu ta hanyar cewa abinda suka yi bai saba da doka ba, kuma ya zama lallai domin kare Amurka daga wasu hare- haren.

Kungiyar dai ta ce gazawa wajen aiwatar da binciken zai rage kimar da Amurka ke da shi wajen matsawa kan tabbatar da gabatar da aiyukan Gwamnati dalla- dalla da take ikirarin yi a Kasashe kamar su Libya da Sri lanka.