Dattawan Borno sun koka da JTF

Gwamnatin jihar borno ta bukaci jami'an tsaron da ke aikin tabbatar da tsaro a jihar da su rinka yin taka tsan-tsan wajen gudanar da ayyukansu ba tare da keta hakkin biladama ba.

Gwamnatin ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwar da ta fitar a yau dangane da yanayin tsaron da ake ciki a Jihar.

A bangare guda kuma Kungiyar Dattawan Jihar Borno ta yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta janye sojojin daga birnin, bisa zargin da ta ke na cewar suna cin zarafi da kashe wadanda ba su jiba basu gani ba.

Sai dai Rundunar Hadin Gwiwar Samar da Tsaron - JTF -- ta musanta dukkanin zargin da ake yiwa jami'anta a wata sanarwar da ita ma ta fitar ga manema labarai da marecen yau