Fari a kusurwar Afrika: Somaliya na kara samun agaji

Image caption Somalia na fama da karancin abinci, saboda fari

Wata kungiyar bada agajin Islama, ta fara raba agaji a babban birnin Somaliya wato Mogadishu bayan da kungiyar al-Shabab ta dage dakatarwar da tayi na hana shigowa da agaji.

Somaliya ce kasar da fari ta fi shafa a kusurwar Afrika bayan tashin hankali na tsawon shekaru 20 a kasar.

Hukumar dakin kan Islama ta OIC ta bada busheshen abinci kamar masar ga dubban mutanen da suka kauracewa birnin kwananan.

Wani jami'in OIC na bukaji sauran kungiyoyin agaji da su dawo aiki Somalia.

Kusan mutane miliyan goma ne dai farin ya shafa a kusurwar Afrika kusan shekaru sittin da suka wuce.

Kusan mutane dubu uku ne ke kaura a kullum daga Somalia zuwa Kenya ko kuma Habasha domin neman taimako.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Somalia Mark Bowden yana birnin Mogadishu domin nazarin yadda rashin abinci ya haddasa matsala a kasar da kuma irin taimakon da za'a bada.

A karshen mako ne dai shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Cif Antonio Guterres ya bukaci kungiyoyin bada agaji da su shiga Somalia domin taimakawa wadanda fari ya shafa.

Fari a kusurwar Afrika ya haddasa karanci abinci a kasashe kamar su Kenya da Habasha da Djibouti da kuma Somalia.