Rupert Murdoch zai bayyana gaban majalisa

Rupert Murdoch Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rupert Murdoch

Bayan kwanakin da aka kwashe Rupert Murdoch na fuskantar matsalin lambar da ba a taba ganin irinta ba.

Dangane da zargin wasu 'yan jaridar dake masa aiki da aikata ba daidai ba-- majalisar dokokin Birtaniya zata yi muhawara kan kiran da ake yi cewar ya janye sunan kampaninsa na News Corporation daga jerin masu son sayen tashar talabijin ta BSkyB.

Jam'iyyar adawa ta Labour ce ta gabatar da kudirin, kuma gwamnati ta ce zata goyi baya.

wakilin BBC ya ce hakan na nufin tana kasa-tana-dabo, game da yuwuwar Rupert Murdoch ya mallaki kampanin BSkyB, domin bisa dukkan alamu a gobe, Laraba, majalisar zata amince da kudirin dake kiran a dakatar da shirin baki daya.