Shugaba Obama ya tattauna da 'yan jam'iyyar Republicans

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mr Ben Bernanke

Shugaban Amurka Barack Obama ya tattauna da 'yan jam'iyyar adawa ta Republicans, domin duba hanyar da za a bi a shawo kan matsalar bashin da ya yiwa kasar dabaibayi.

Bayan kwana da kwanaki ana irin wannan tattaunawa, an ruwaito wani 'dan jam'iyyar Republican din ya ambato Mr Obama na cewa ya gaji da kai komo kan wannan batu.

Shugaban babban bankin Amurka Ben Bernanke, ya ce tattaunawar ta Amurka ta shafi duniya baki daya.

A cewarsa idan har basussuka suka sanya kasar ta durkushe, to zai zamanto babbar matsala , saboda ana ganin baitul malin Amurka a matsayin wanda ya fi ko wanne kariya a duniya, don haka rushewarsa zai sanya tashin hankali a daukacin tsarin kudi na duniya .