shugabar Jamus ta kai ziyara zuwa Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban kasar Nigeria Goodluck Jonathan

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela ta isa Najeriya a ci gaba da rangadin da take yi a wasu kasashen nahiyar Afirka. Wannan ne karon farko da wani shugaban gwamnatin Jamus ya kai irin wannan ziyara Najeriya cikin shekaru talatin din da suka wuce.

A daren jiya ne ta iso bayanda ta yada zango a kasashen Kenya da Angola.

Ana sa ran za ta gana da shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan da kuma Kungiyar `yan kasuwan kasar da ke hulda da kasar Jamus a lokacin ziyarar tata.

Bugu da kari ana ganin ziyarar zata karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu ta fuskar kasuwanci da kuma diplomasiya.

Rabon Nigeria da karban bakwuncin irin wanan babbar 'bakuwa daga kasar Jamus dai tun daga shekerar 1976 lokacin da shugaba Helmut Smith ya ziyarci Nigeriyar.