Mutane 17 sun mutu a harin bama-bamai a Indiya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mumbai tayi fama da harin bam a kwanakin baya

A kai harin bam guda uku a babban birnin kasuwancin Indiya wato Mumbai.

Akalla mutane goma sha bakwai ne suka mutu a sanadiyar tashin bama-baman a yayinda da dama suka jikkata.

Daya daga cikin harin an kai shine a cikin garin sannan sauran anyi su ne a kudancin garin.

Duka bama-baman biyu dai sun tashi ne a dai dai lokacin da ake ribibin komawa gida.

Mahukanta a kasar sun alakanta harin da ta'adancin.