Badakalar satar bayanan wayoyi a Amurka

Image caption Rupert Murdoch

Manyan 'yan jam'iyyun Republicans da Democrats a majalisar dokokin Amurka sun yi kira a gudanar da bincike a'kan 'ko yuwar satar bayanan wayoyin salula daga wurin kamfanin News of the World ya sabama dokokin kasar.

Sun ce zargin da ake akancewa manema labarun kamfanin sun biya jami'an yansandan Birtaniya kudi, me yuwa ya sabama dokokin Amurka na yaki da rashawa , abun da kuma ya shafi uwar kamfanin News international dake Amurka wato News corporation.

Senatocin sun yi kira ga hukumar FBI akan ta gudanar da bincike akan 'ko manema labarun sun karya dokokin saurare ko karanta sokonin wayoyin Amurkawa.

Sun kuma yi kira ga hukumar shari'ar kasar da ta gudanar da bincike akan zargin biyan 'yansandan Birtaniya kudi.

Rahotanni sun ce ana zargin kamfanin News of the world ya nemi wani jami'in 'yansanda a Newyork inda ya yi yunkurin sayen bayanan wayoyin mutane da suka mutu a hare haren ranar tara ga watan satumba ta shekerar 2001.