An kai harin bam a wani masallaci a Kandahar

Wani harin bam da akai kai a wani masallaci a kudancin Afghanistan inda ake zaman makokin dan uwan shugaba Hamid Karzai, ya kashe mutane uku.

Wasu rahotanni sun ce dan kunar bakin waken ya tayar da bam din da ya boye a cikin rawaninsa ne a lokacin da aka dakatar da shi a kofar shiga cikin masallacin.

Yayin da wasu kuma suka ce dama yana hakon wani babban malami ne, Hekmatullah Hekmat, shugaban majalisar Islama ta lardin Kandahar, wanda ke daya daga cikin wadanda suka rasa rayukan nasu.

'Yan uwan shugaba Karzai hudu ne tare da gwamnan Kandahar ke cikin masalllacin a lokacin da aka kai harin, amma ba su samu ko da kwarzane ba. Wakilin BBC, ya ce," Majalisar dinkin duniya ta ce hare-haran kunar bakin wake sun taimaka wajen karuwar fararen hular da ake kashewa, inda aka kashe fararen hula dubu daya da dari hudu da sittin da biyu a cikin watanni shidan da suka wuce."