Merkel ta gana da Goodluck a Abuja

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi wata tattaunawa tare da Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya a kan hanyar da za su iya bunkasa hadin kai dake tsakaninsu.

Batutuwan da suka tattaunawa sun hada da harkokin noma da masana`antu da makamashi da kuma kasuwanci.

Shugabannin biyu sun kuma jaddada makamaci a matsayin wani na musamman da za a mayar da hankali a kai.

Shugabar Gwamnatin Jamus din da aka yiwa marhabin da wani bukin soji a fadar shugaban kasa a Abuja, ta yi amfani da damar wajen gayyatar Shugaba Goodluck zuwa Jamus a cikin shekara mai zuwa.

Da take magana game da matsalar tsaro a Najeriyar, Ms Merkel ta ce yana da muhimmanci Najeriya ta samu nasara wajen yaki da tashe tashen hankalu da kuma ta'addanci a cikin kasar.

Sannan kuma ta bayyana cewar tabbatar da mutunta kare hakkin bil adama nada muhimmancin gaske a kasar.

Ana sa ran Merkel ta bar Najeriya a yau bayan ta bude wani taron yan kasuwar Najeriya da Jamus , tare kuma da ganawa da Shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yankin yammacin Afrika ta ECOWAS a Abuja.