An bada sammacin Rupert Murdoch

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Hashakin mai kudi, Rupert Murdoch

Wani kwamitin majalisar dokokin Birtaniya ya fitar da sammacin neman hamshakin mai kamfanin kafofin yada labara,Rupert Murdoch da dansa James.

Kwamitin ya neme su ne su gurfana a gabansa domin amsa tambayoyi kan rikicin da ake na satar sauraro da kallon sakon wayoyin jama'a.

An yanke shawarar fitar da sammacin ne bayan da mutanan biyu suka ce ba za su bayyana a gaban kwamitin ba makon gobe. Babbar editar kamfanin News International a nan Birtaniya, Rebekah Brooks, ta ce zata je wajen sauraran bahasin.

Har yanzu 'yan majalisar ba su san abin da zai faru ba indan har wannan lokacin mutanan biyu suka ki zuwa majalisar dokokin.

Yanzu haka 'yan sandan dake binciken zarge zargen satar sauraro da kallan sakwannin wayar mutane sun kama wani tsohon mataimakin editan jaridar News of the World wadda aka rufe akan batun.