Dubban masu zanga zanga sun yi maci a kasar Guinea Bissau

Pira Ministan Guinea Bissau
Image caption Pira Ministan Guinea Bissau

Dubban masu zanga zanga sun yi maci ta cikin Bissau, babban birnin kasar Guinea Bissau, suna kira ga Pira ministan kasar, Carlos Gomes Junior da ya sauka. Masu zanga zangar na zargin sa ne da hana a gudanar da bincike sosai kan abinda suka kwatanta a matsayin kashe kashen siyasa.

Har ila yau kuma sun ce pira ministan bai yi wani abun azo a gani ba domin karesu daga tsadar abincin da suke fuskanta.