Amurka zata kai kayan agaji Somalia

Matsalar yinwa a Somalia Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Matsalar yinwa a Somalia

Amurka ta ce za ta bari a kai agajinta zuwa yankunan da ke hannun kungiyar Al shabbab mai kishin Islama a Somalia, matukar abin ba zai amfani masu fafitikar ba.

Wani jami'in hukumar ba da agaji ta Amurkar, USAID ta tana bukatar tabbacin Majalisar Dinkin duniya da kungiyoyin agaji cewa ba za su dinga biyan haraji ga kungiyar al Shabbaab ba. Kungiyar ta Al shabbab ce ke rike da yanki mai yawa da ake fama da yinwa a kasar.