Dr. Goodluck ya gana da dattawan Borno

Tashin hankali a Maiduguri
Image caption Tashin hankali a Maiduguri

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya gana da `yan majalisar tarayya, da wasu dattawa daga jihar Borno, sannan kuma da wakilan kungiyar Tuntunbar Juna ta dattawan arewa, wato ACF, don duba hanyoyin shawo kan rikicin boko haram.

Wasu daga cikin shawarwarin da suka bayar sun hada da bukatar janye sojoji daga garin Maiduguri, da kuma tattaunawa da `yan Kungiyar ta Boko Haram.

Sai dai gwamnatin tarayya ta ce ba za'a janye sojoji daga garin Maiduguri ba tukunna