Wasu bakuna a Turai na fuskantar matsaloli

Image caption Kudaden Turai

Hukumar dake sa ido akan bankuna a Turai tace, akwai bankuna takwas na kasashen Turan da basu da karfin jurewa matsalolin kudi.

Anyi bincike ne dai akan bankuna casa'in, sai dai kuma bankuna biyar a Spain da kuma biyu a Girka, da kuma daya a kasar Austria ne basu tsallake gwajin da aka yi ba.

Dan haka ne ma shugaban kungiyar tarayyar Turai, Herman an Rompuy ya kira wani taron gaggawa da shugabannin kasashen dake amfani da kudin Euro sha bakwai mako mai zuwa

Shugaban yace za'a yi taron ne domin tattauna yadda za'a bullowa matsalolin tattalin arzikin kasashen dake amfani da kudin Euro da kuma batun tallafi ga kasar Girka.