News corporation yayi taka-tsantsan sosai : inji Murdoch

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rupert Murdoch

Mashahurin attajirin nan kan harkokin sadarwa wato Rupert Murdoch, ya ce yayi imanin cewa kamfaninsa na News Corporation, yayi takatsantsan sosai akan badakalar satar shiga wayoyin mutane da zarginda ake masa na aikata ba daidai ba a Birtaniya.

A wata hira da yayi da daya daga cikin jaridunsa, wato Wall Street Journal, Mr Murdoch ya bayyana cewa kamfanin News Corp yayi wasu kananan kurakurai ne, kuma nan ba da jimawa ba zai sake farfadowa.

Tuni dai Mr Murdoch da 'dansa James suka amince su bayyana a gaban wani kwamiti a majalisar dokokin Birtaniya a makon gobe domin amsa laifukan da ake zarginsu da yi, wadanda suka musanta.

Hakazalika hukumar 'yan sanda dake gudanar da bincike a Amurka wato FBI ta fara wani bincike kan zarge zargen cewa, kamfanin News Corporation , ya nemi ya saci hanyar sauraro da kallon sakwannin wayoyin wadanda harin sha daya ga watan Satumba ya shafa, a biranen New York da Washington shekaru goma da suka gabata.

Wasu yan siyasar Amurka ne suka nemi da a gudanar da binciken.