Rupert Murdoch ya mika sakon neman afuwa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Rupert Murdoch

Hamshakin attajirin nan mai kafafen yada labarai, Rupert Murdoch ya mika sakon neman afuwa ga iyalan yarinyar nan 'yar makaranta da aka kashe wacce kuma kamfanin jaridarsa ya saci bayanai daga wayarta.

Kamfaninsa, wato News International ya kuma ce, Mista Murdoch zai kuma yi amfani da sakon da zai sanya a jaridun Birtaniya wajen nuna nadama dangane da abinda ya kira aikata ba daidai ba da aka yi.

Ya ce: "A matsayi na na wanda ya kafa wannan kamfani nayi nadama, kuma na nemi afuwa dangane da abinda ya auku."

A wani labarin kuma Shugabar Jaridar News International a Burtaniya Rebekah Brooks ta ajiye aikinta.

Rebekah dai na fuskantar matsin lamba ne saboda badakalar satar bayanai ta wayar salula da kamfanin jaridar News of the World ta yi wadda ta taba zama editan ta har zuwa shekarar 2003.

An dai zargi jaridar ne da satar bayanan wata yarinyar makaranta da aka kashe, Milly Dowler a lokacin da Ms Brooks take editan jaridar.

To sai dai Ms Brooks ta musanta cewa tana da masaniya game da batun, kuma wanda ke da mallakin jaridar Rupert Murdoch ya bata goyon bayan.

A wani sakon email da ta aikawa ma'aikatan jaridar, Ms Brooks ta ce ta sauka ne domin kada zamanta ya karkatarda hankalin kan kokarin da Jaridar News International take yi na dawo da martabar jaridar.