Rebekah Brooks ta sauka daga mukaminta

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rebekah Brooks

Shugabar Jaridar News International a Burtaniya Rebekah Brooks ta ajiye aikinta.

Rebekah dai na fuskantar matsin lamba ne saboda badakalar satar bayanai ta wayar salula da kamfanin jaridar News of the World ta yi wadda ta taba zama editan ta har zuwa shekarar 2003.

An dai zargi jaridar ne da satar bayanan wata yarinyar makaranta da aka kashe, Milly Dowler a lokacin da Ms Brooks take editan jaridar.

To sai dai Ms Brooks ta musanta cewa tana da masaniya game da batun, kuma wanda ke da mallakin jaridar Rupert Murdoch ya bata goyon bayan.

A wani sakon email da ta aikawa ma'aikatan jaridar, Ms Brooks ta ce ta sauka ne domin kada zamanta ya karkatarda hankalin kan kokarin da Jaridar News International take yi na dawo da martabar jaridar.