Hafsan Hafsoshin Turkiyya ya yi murabus

Hafsan Hafsoshin Turkiyya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hafsan Hafsoshin Turkiyya

Hafsan hafsoshin sojojin Turkiyya, da hafsoshin sojin ruwa, dana kasa da na sama duk sunyi murabus.

Murabus din nasu sun biyo bayan karin kace nacen da ake yi tsakanin sojin kasar da gwamnatin kasar mai raba addini da siyasa.

Masu aiko da rohotonni sunce shara'ar da ake yiwa wasu manyan hafsan sojoji ne ta kara zafafa tankiyar dake tsakanin gwamnati da rundunar sojin