Shugaba Hugo Chavez zai koma Cuba

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Hugo Chavez

Shugaban kasar Venezeula Hugo Chavez ya nemi izinin komawa Cuba daga wurin Majlisar dokoki kasar domin samun karin kulawar data kamata dangane da cutar cancer da yake fama da ita.

Mr Chavez ya shafe kasa da makoni biyu a Venezuela bayan da ya shafe kusa da wata daya baya kasar.

A jawabin da ya gabatar a Majalisar dokokin Venezeula ta wata kafar talibin ta gwamnati shugaba Chavez ya ce zai fara karban magani zagaye na biyo da ake kira chemotheraphy kuma yana son ya koma Cuba a yau asabar.

Sai dai be ce komai ba akan tsawon lokacin da zai zauna a birnin Havana.

Mr Chavez ya fara rashin lafiya ne a lokacin da ya kai ziyara zuwa Cuba a farkon watan yuni.

An dai shafe makoni na rashin tabas biyo bayan bayan kasancewarsa a kasar kuma ba'a fitar da wani cikaken bayani ba akan halin da yake ciki ga jama'ar kasar.