Rupert Murdoch ya nemi afuwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rupert Murdoch

Hamshakin attajirin nan kan sadarwa wato Rupert Mudoch ya nemi afuwa daga wurin jama'ar Birtaniya kan ayyukan jaridarsa, wato News of the World.

A jerin talar da aka buga a cikin jaridu mai taken ' kuyi hakuri' wanda Mr murdoch ya rataba hanu akai, ya ce yana neman afuwa kan babban laifi da kuma halin da aka jefa rayuwar mutanen da wanan abu ya shafa.

A cikin wasikar, Mr Murdoch ya ce kamfanin News International zai dauki karin wasu matakai domin shawo kan batutuwan da badakalar satar bayanan wayoyin jama'a ta janyo.

A jiya juma'a ne Mr Murdoch ya gana da iyalan Milly Dowler wato yar makarantar da aka kashe wadda jaridar News of the world ta saci bayanan wayarta a shekerar 2002.

Talacen talacen da za'a wallafa zagaye na biyu a karshen makon da muke ciki zasu jadada alkawarin da Mr Murdoch yayi na bada hadin kai kwamitn bincike na 'yansanda da kuma diyyar da za'a wadanda abun ya shafa.