Rupert Murdoch ya nemi afuwa ga jama'ar Birtaniya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rupert Murdoch

Hamshakin attajirin nan mamallakin kafofin yada labarai, Rupert Murdoch ya ce, baiji dadin abun da ya kira babban kuskure da aka yi ba a jaridarsa ta News of the World wadda ta saci bayani da sakonnin mutane ta waya.

Mr Murdoch ya sayi shafuka a jaridun Birtaniya da dama inda ya sanya sakon neman gafara dauke da sa hannunsa.

Ya ce, aikin jaridar News of the World ne ganin cewa wasu sunyi aiki da doka, amma sai ga mai dokar barci ya buge da gyangyadi.

A jiya Mr Murdoch ya gana da iyalan Milly Dowler wato yar makarantar da aka kashe wadda jaridar News of the world ta saci bayanan wayarta a shekera ta dubu biyu da biyu.

Talacen talacen da za'a wallafa zagaye na biyu a karshen makon da muke ciki za su jaddada alkawarin da Mr Murdoch yayi na bada hadin kai ga kwamitin bincike na 'yansanda da kuma diyyar da za'a wadanda abun ya shafa.