Sojin Najeriya na yin kisan kan mai tsautsayi -Inji Kungiyar Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta zargi rundunar sojin Nigeria da aikata kisan ba rarrabewa a yakin da take yi da kungiyar 'yan gwagwarmayar Islaman nan a arewacin kasar.

Kungiyar ta Amnesty ta ce, ta yi imanin cewa mutane 25 ne, harda mata da yara aka hallaka a wani artabu da sojoji sukayi da 'yan boko haram mako guda da ya wuce.

Wannan dai ya ninka adadin da rundunar sojin ta bayar.

Wakilin BBC ya ce a watanni biyun da suka wuce a kara yawan dakarun da ake dasu arewa masu gabasin Nigeria, amma kuma harkar tsaro sai kara tabarbarewa ta ke yi.

Rundunar tabbatar da tsaro a yankin ta ce mutane na gama baki da kungiyar ta Boko Haram, abinda ke sa aikin sojin ya kara zama mai wuyar gaske. Ana dai zargin kungiyar da jerin hare hare a yankin Maiduguri.