Taron sanin makamar aiki na ministocin Nigeria

Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

A Najeriya, a yau ne aka shiga rana ta biyu a bitar sanin makamar aiki da gwamnati ke yi ga ministoci da masu baiwa shugaban kasa shawara.

Bitar wadda shugaban kasar ya bude, ta tabo bangarori da dama wadanda suka shafi yadda mahalartata za su tafiyar da sha'anin gwamnati ganin irin kalubalen da ke fuskantar kasar.

Shi dai shugaban kasar Dakta Goodluck Jonathan ya rantsar da ministoci guda arba'in, da masu bashi shawara da dama don gudanar da ayyukan ci gaban kasa.

Sai dai 'yan kasar na suka kan yadda gwamnatin ke ware makudan kudade kan ministocin da masu baiwa shugaban kasar shawara, maimakon yin amfanin da irin wadannan kudade don ci gaban kasa.