Shugaban Venezuela ya fice daga kasar

Mista Chavez ya tafi Cuba Hakkin mallakar hoto Other
Image caption Shugaban Venezuela, Hugo Chavez

Shugaban kasar Venezuela, Hugo Chavez, ya bar kasar zuwa Cuba domin a sake yi masa magani na cutar daji wato Cancer.

Gabanin tafiyar Mista Chavez, likitoci sun ce babu wasu kwayoyin cuta a jikinsa wadanda za su yi masa illa bayan da aka cire wani hakki daga jikinsa a watan jiya.

Tun da farko a jiya Asabar ne Mista Chavez ya mika wasu daga cikin dawainiyar tafiyar da mulkin kasar ga mataimakinsa da kuma ministan Ma'aikatar Kudi.

Sai dai ya yi watsi da kiraye- kirayen da 'yan adawa ke yi kan ya mika dukkan ragamar mulkin kasar ga mataimakinsa matukar baya kasar.

A watan jiya ne dai likitoci a Cuba suka gudanar da tiyata kan Shugaba Chavez, bayan da aka gano cewa yana dauke da ciwon daji.