Wani minista ya sauka daga mukaminsa a Masar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu gudanar da zanga-zanga a Masar

Ministan harkokin wajen Masar Mohammed el-Orabi, ya sauka daga kan mukaminsa gabanin wani garabawul na mukarraban gwamnati da za a sanar a yau Lahadi.

Firayim Ministan kasar, Essam Sharaf ya yi alkawarin yin garabawul ga gwamnatinsa a dai-dai lokacin da ake ci gaba da zanga-zanga a birni Alkahira saboda rashin aiwatar da sauye-sauyen da gwamnati ta yi alkawarin gudanawarwa cikin gaggawa.

A watannin baya ne dai 'yan kasar suka tilastawa tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak sauka daga kan mulki bayan da ya kwashe fiye da shekaru talatin a kan mulkin.

Hakan ne ya baiwa sojojin damar karbar ragamar mulki sannan suka yi alkawarin gudanar da sauye-sauye a kasar.