Shugaban 'yan sandan London ya yi murabus

Hedikwatar yansandan London
Image caption Hedikwatar yansandan London

Shugaban rundunar 'yan sanda a London Sir Paul Stevenson ya ajiye aikinsa saboda an alakanta shi da aka yi da abun kunyan nan na satar bayanan jama'a ta waya da yaci jaridar News of the World.

Sir Paul yace ya ajjiye aikinsa ne saboda zargin cewa yana da alaka da komfanin jaridar Mupert Murdoch wanda abun kunyan nan ya dabaibaye.

Tun farko dai 'Yan Sanda sun tsare Rebekkah Brooks wadda ta ajiye aikinta a matsayin shugabar kamfanin News Inaternational na hamshakin attajirin nan Rupert Murdoch.

Tsare ta nada nasaba ne da binciken zargin satar sakonni ta waya da cin hanci da rashawa da ake yiwa 'yan jaridar kamfanin.

Ita ce jami'a mafi girman mukami da aka cafke kawo yanzu a abun kunyan nan da ya ci Jaridar News of the World.

Wakilin BBC ya ce, Rebekkah Brooks na da kusanci sosai da manya a Burtaniya, cikinsu har da Firayim Minista David Cameroon .