'Yan tawayen Libiya sun killace garin Brega'.

'Yan tawayen Libiya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan tawayen Libiya

Shugabannin 'yan tawaye a Libiya sun shaidawa BBC cewa, dakarun dake yaki da na Kanar Gaddafi, kusan su ke iko da galibin garin Brega.

Wannan gari mai arzikin mai, a karo da dama bangarorin biyu na kama shi, yana kuma subuce masu, tun bayan fara bore ga gwamnatin Kanar Mu'ammar Gaddafi.

Wani kakakin 'yan tawaye ya shaida wa BBC cewa, 'yan tawayen suna wajen garin saboda yawan nakiyoyin da sojin gwamnatin Gaddafi suka daddasa.

'Yan tawayen suka ce dakarun gwamnati suna ja da baya zuwa yamma.

Gwamnatin Libiyar dai ta musanta dukan ikirarin.

Ta jaddada cewa har yanzu garin Brega a hannunta yake, sannan ta kashe 'yan tawayen fiye da 500 a can din.