'Ya kamata Najeriya ta yi taka-tsan-tsan'

Ya kamata Najeriya ta yi taka-tsan-tsan
Image caption Shugaban Nijar, Muhammadu Isoufou

Gwamnatin Nijar ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su yi taka tsan-tsan wajen daukar matakan korar 'yan kasar daga Najeriya.

A kalla 'yan Nijar tamanin da uku ne Najeriyar ta kora a kwanakin da suka gabata sakamakon kalubalen tsaro da ake fuskanta a kasar biyo bayan hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram ke ikirarin kaiwa a wasu sassan kasar.

Sai dai hukumomin Nijar din sun ce bai kamata Najeriyar ta rika korar 'yan kasarta ba, ba tare da gudanar da cikakken bincike ba.

Ministan harkokin wajen Nijar Malam Bazun Muhammed wanda ya yi wannan kira, ya ce za su gana da shugabannin Najeriya a game da batun.