Bama-bamai sun sake tashi a Maiduguri

Image caption Irin barnar da bam ya yi a Maiduguri

Rahotannin da muka samu daga Maiduguri babban birnin jihar Borno sun nuna cewar an sake samun tashin bom da safiyar yau a kusa da sha tale talen unguwar Bulunkutu dake gefen birnin.

Bom din dai ya tashi da motar dake dauke da wasu jami’an Rundunar Hadin Gwiwar samar da tsaro JTF wanda yayi sanadiyyar jikkatar wasu jami’an tsaro uku.

Ko a ranar Juma’ar da ta gabata said a aka samu harin bom kan motar jami’an tsaron a daidai wannan sha tale-tale na Bulunkutu wanda ya jikkata jami’an yansanda biyar.

Rundunar ta JTF ta bayyana cafke mutane shida da take zargi da kai harin bom din na safiyar yau.

Birnin na Maiduguri dai na fama da matsalolin tsaro, musamman wadanda suka shafi hare-haren bama-bamai da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram na kaiwa.

A nasu bangaren hukumomi a jihar sun yi kira ga 'yan kungiyar su amince da tayin sasantawar da gwamnati ta yi musu.