Murdoch ya ce ba shi da alhakin aikata abun kunya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rupert Murdoch da dansa James

Hamshakin attajirin nan mai kafafen yada labarai Rupert Murdoch tare da dansa ,James sun bayyana a gaban kwamitin majalisar dokokin Birtaniya.

Kwamitin na bincike ne kan zargin da ake yi wa wasu ma'aikatansa na satar karanta ko sauraren sakonni a wayoyin jama'a. Mr Murdoch dai ya ce ba shi ke da alhakin aikata wannan abin kunya ba.

Ya ce duk da haka ya girgiza kwarai da ya ji labarin cewa jaridarsa ta News of the World ta yi satar karanta sakonni a wayar wata yarinya yar makaranta da aka kashe.

Shi da dan nasa duk sun nemi gafara kan abin da ya farun.

Daga baya kuma 'yan majalisar sun yi rambayoyi ga shugabar kamfanin Mr Murdoch a nan Biritaniya, Rebekkah Brooks.

Misiz Brooks - wadda ta taba zama editar jaridar tasa ta News of the World, wadda 'yan sanda suka kama makon jiya, ta ba da nata hakurin a kan wadanda jaridar ta yi wa ba daidai ba wajen satar sauraro da kallon sakonnin wayoyinsu.

Ta ce ita da sauran shugabannin kamfanin sun dauki mataki cikin hanzarin kai tsaye bayan da suka sami bayanin satar saurare da kallon sakoonin.

Amma kuma daga baya ta saba wa wannan zance nata, yayin da ta ce kamfanin bai yi sauri ba wajen daukar mataki.

Ga wasu yan majalisa dai wata dama ce ta turke Rupert Murdoch, wanda suke yi ma kallon mai matukar fada aji ta fuskar siyasa, ta hanyar amfani da jaridunsa.