Ma'aikata a Najeriya na yajin aiki

Gamayyar kungiyoyin kwadago a Nigeria sun ce, suna kan bakansu dangane da soma yajin aikin gargadi na kwanaki uku da za a soma daga sha biyun daren yau.

Kungiyoyin kwadagon sun ce koda gwamnoni sun amince su biya sabon tsarin albashin ba zasu fasa yin yajin aikin ba.

Su dai kungiyoyin kwadagon suna so ne a soma biyansu mafi karancin albashi dubu goma sha takwas daga watan Maris ba tare da wani sharadi ba.

Tun daga makon jiya ne dai ake ta tattaunawa tsakanin gwamnati da kuma kungiyoyin kwadagon.