Bala'in yunwa a wasu sassa na Somalia

Hukumomi na shirin shelar cewa bala'in yunwa ya afka ma wasu sassa na Somalia.

Mutane kimanin miliyan goma ne a yankin gabashin Afrika ke fama da matsalar fari, mafi muni cikin shekaru sama da hamsin.

A gobe ake sa ran Majalisar Dinkin Duniya zata bada sanarwar cewa yanayin ya kara tabarbarewa, ta yadda za a iya cewa bala'in yunwa ya sake afka ma yankin a karon farko cikin shekaru goma sha tara.